Afirka

An Fidda Gawakin Yan Gudun Hijira 74 A Gabar Tekun Medeteranian A Kasar Libya

Kungiyar Red Cresen ta bada agaji a kasar Libya ta bada sanarwan cewa ta gano gawakin yan gudun hijira masu kokarin tsallaka tekun Medeteranian zuwa tarayyar Turai.

Kokarin Gwamnatin Congo na kalubalantar matsalar tsaro

Ministan cikin gida da tsaro na kasar Demokaradiyar Congo ya bukaci daukan matakan warware rikicin kasar ta hanyar Siyasa maimako shigar Jami'an 'yan sanda.

Bukatar taimako na Gwamnatin Kenya domin kalubalantar Fari a kasar

Gwamnatin kasar Kenya ta bukaci taimakon kungiyoyin kasa da kasa domin kalubalantar matsalar fari da kasar ke fuskanta.

Guinea : An Kashe Mutane Biyar A Cikin Masu Zanga-zanga

Rahotannin daga Guinea na cewa a kalla mutane biyar ne suka mutu a yayin zanga-zangar neman sake bude azuzuwa a Conakry babban birnin kasar.