Dec 16, 2016 17:13 UTC
  • Riek Machar Ya Musanta Cewa Yana Tsare A Kasar Afirka Ta Kudu

Madugun 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu Riek Machar ya musanta labarin da ke cewa mahukunta a kasar Afirka ta Kudu na tsare da shi a birnin Pretoria inda ya ce hakan wata farfaganda ce kawai da gwamnatin Sudan ta Kudu take yadawa.

A wata sanarwa da jam'iyyar 'yan tawayen ta fitar, jam'iyyar ta zargi gwamnatin Shugaba Silva Kirr na kasar Sudan ta Kudun da yada wannan labarin a matsayin wata hanyar farfaganda da bakanta fuskar Mr. Machar ta hanyar hada baki da wasu kafafen watsa labarai.

Sanarwar ta zargi gwamnatin da cewa ita ce ta kirkiri wannan labarin tana mai cewa gwamnatin Sudan ta Kudun tana tsammanin kowace gwamnatin tamkar irin nata ne da ta karen tsaye ga dokokin kasa, tana mai cewa ko da ma a ce ana tsare da Mr. Machar ne, hakan ba zai sauya tafarkin rikicin da ke gudana a kasar ba.

A shekaran jiya Talata ce kamfanin dillancin labaran Reuters ya ba da rahoton cewa Mr. Machar wanda ya gudu daga kasar Sudan ta Kudu a watan Augustan da ya gabata, yana tsare a kasar Afirka ta Kudu don hana shi ci gaba da ruruta wutar yakin basasan da ke gudanar a jaririyar kasar Sudan ta Kudun.

Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ce wasu majiyoyin gwamnatin Afirka ta Kudu na daban sun shaida masa cewa Mr. Machar din yana a matsayin bakon gwamnatin Afirka ta Kudun ne amma ba wai ana tsare da shi ba ne.

 

Tags

Ra'ayi