Dec 23, 2016 07:55 UTC
  • An Ji Karara Fashewa A Birnin Acra Na Kasar Ghana A Safiyar Yau Jumma'a

Majiyoyin labarai daga birnin Acra na kasar Ghana sun bayyana cewa an ji karar tashin boma bomai masu ban tsaro a wata unguwa cike da ofisoshin kungiyoyon kasa da kasa

Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto majiyoyin asbitoci a birnin suna bayyana cewa manya manyan boma bomai sun tashi a wata unguwa inda wasu ofisoshin kungiyoyin kasa da kasa da dama suke, kuma ya zuwa lokacin bada wannan labarin mutane kimani 7 ne aka tabbatar da mutuwarsu, a yayin da wasu 12 kuma suka ji rauni.

Labarin ya kara da cewa kungiyoyin bada agaji suna cikin aikin gano wadanda suke da sauran numfashi sanadiyar tashe tashen boma bomai, don haka akwai yiyuwan yawan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata ya karu.

Kasar Ghana dai ta kammala zabubbukan shugaban kasa da na majalisun dokokin kasar cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ranar 7 ga watan Decemban da muke ciki, kuma tuni hukumar zaben kasar ta tabbatar da Nana Akofo Addo na babbar jam'iyyar hamayyar kasar a matsayin wanda ya lashe zamen shugaban kasa, banda haka shugaban kasa mai ci John Dramani mahama ya amince da sakamakon zaben. 

Tags

Ra'ayi