• Gambia : Jammeh Ya Kori Minista Da Jakadun Kasarsa 12

A Gambia, a yayin da wasu shugabannin kasashen yammacin Afrika suka yanke shawara sake komawa kasar domin lallashin Shugaba Yahya Jameh ya mika mulki a ranar 19 ga watan nan, Shugaba Jammeh ya kori ministan sadarwansa da kuma wasu jakadun kasarsa 12 dake ketare.

Rahotannin sun ce an kori jami'an ne saboda taya Adama Barrow murna kan nasara da yayi a zaben shugabancin kasar na ranar 1 ga watan Disamban shekarar da ta gabata.

Jakadun da aka sallama sun hada dana kasar dake Amurka, Senegal, MDD, Sin, Rasha, Biritaniya, Turkiyya, Belgium, Spain, Cuba, Guinea-Bissau da kuma Habasha.

Kasar Gambia dai ta shiga halin rashin tabas ne tun bayan da shugaban kasar Yahya Jammeh dake shugabancin kasar tun shekara 1994, ya sanar da kin amincewa da shan kaye a zaben shugabancin kasar, mako guda bayan da ya taya abokin hammayarsa Adama Barrow murna kan nasara lashe zaben.

Kuma bayan hakan ne shugaba Jammeh ya garzaya kotu saboda a cewarsa an tafka kura-kurai a zaben.

Jiya Litinin ne dai ya kamata alkalan da ake akayo hayarsu daga Najeriya da Saliyo su yi zamen sauraren kara saidai ba ko daya daga cikinsu daya isa kasar ta Gambia.

Hakazalika a ranar Litinin din ce wasu shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS / CEDEAO sukayi wani taro a Abuja babban birnin tarayya Najeriya inda suka amince da tura wata tawaga data kunshi shugaba Muhamadu Buhari Na Najeriya, Shugabar kasar Laberia kana shugabar kungiyar ECOWAS, Ellen Johnson Sirleaf da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama domin lallashin Jammeh ya mika mulki cikin ruwan sanyi.

Jan 10, 2017 06:35 UTC
Ra'ayi