• Libya Ta Gayyaci Jami'an Sojin Kasar Rasha Zuwa Tripoli

Gwamnatin hadaka ta kasar Libya ta gayyaci wasu daga cikin manyan jami'an sojin kasar Rashar zuwa Tripoli, domin taimaka ma kasar Libya da shawarwari da kuma dubaru na yaki da 'yan ta'adda.

Shugaban majalisar shugabancin kasar Libya Akila Salih ne ya bayyana hakan, inda ya ce sun tattauna wannan batu tare da mahukuntan kasar kasar a yayin ziyarar da ya kai birnin Moscow a cikin watan Disamban da ya gabata, inda ya ce Rasha a shirye take ta taimaka ma kasar Libya ta fuskar soji.

Daga cikin abubuwan da gwamnatin kasar Libya ke bukata daga kasar Rasha dai har da bayar da horo ga sojojin kasar Libya kan yaki da ta'addanci, da kuma koyar da su wasu dubaru na musamman ta fuskar aikin soji.

 

Jan 10, 2017 12:05 UTC
Ra'ayi