• Kotun Kolin Gambiya Ta Dage Zaman Sauraren Karar Jammeh Kan Zaben Shugaban Kasa

Kotun kolin kasar Gambiya ta sanar da dage zaman da ta tsara gudanarwa a yau din nan kan karar da shugaban kasar Yahya Jammeh ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar zuwa watan Mayu mai kamawa saboda rashin halartar isassun alkalai.

Rahotanni daga kasar Gambiyan sun bayyana cewar a yau ne kotun ta sanar da wannan mataki cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce saboda rashin halartar alkalan da aka tsara za su saurari karar, don haka an dage ci gaba da sauraren karar har sai watan Mayu mai kamawa lokacin da aka saba alkalan suna zama.

Babban alkalin kasar Gambiy, dan Nijeriya Emmanuel Fagbele ya ce a watan Mayu din dai ana sa ran alakar biyar 'yan kasashen waje daga Nijeriya da Saliyo za su sami damar halartar zaman kotu don gudanar da shari'ar.

Rahotanni sun ce kotun dai ta cika makil da magoya bayan shugaba Jammeh a daya bangaren kuma da magoya bayan 'yan adawan.

Wannnan lamari dai yana zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kungiyar ECOWAS ta tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka karkashin jagoranci shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari suke shirin komawa kasar Gambiyan a gobe Laraba don ganawa da shugaba Jammeh domin lallashinsa da ya mika mulki ranar 19 ga watan Janairun nan ga zababben shugaban kasar Adama Barrow.

A jiya Litinin ne dai wasu shugabannin kasashe a Afirka ta Yamma suka yi wani taro a Abuja, babban birnin Najeriya, kan makomar siyasar Gambiya inda suka yanke shawarar sake tura wata tawaga don ganawa da shugaba Jammeh.

 

Jan 10, 2017 17:04 UTC
Ra'ayi