• An Samu Gawawwakin Wasu Sojojin Kamaru 3 Da Boko Haram Ta Kasashe

Majiyoyin tsaro a kasar Kamaru sun tabbatar da cewa, an samu gawawwakin wasu sojojin kasar da ke aikia cikin rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a cikin yankin Najeriya da ke iyaka da kasar.

Shafin yada labarai na Afirka Time ya bayar da rahoton cewa, majiyoyin ma'aikatar tsaro a kasar kamaru sun sanar da cewa, an samu gawwakin sojojin guda uku ne a cikin yankin Iyawa da ke cikin tarayyar Najeriya a kusa da iyaka da Kamaru.

Kasashen Kamaru, Najeriya, Nijar da kuam Chadi, sun kafa rundunar hadin gwaiwa domin yaki da 'yan kungiyar Boko haram, wadanda suke addabi al'ummomi wadannan kasashe da hare-haren ta'addanci, kuma dukkanin kasashen hudu sun ce an samu gagrumar nasara wajen karya lagon wannan kungiya.

 

Jan 11, 2017 11:18 UTC
Ra'ayi