• Gambiya: An Dage Ziyarar  Shugaban Najeriya Zuwa Gambiya Zuwa Ranar Juma'a:

An dage tafiyar shugaban kasar Najeriya zuwa Gambiya zuwa jibi Juma'a.

Tashar telbijin din France 24 ta bada labarin cewa ziyarar da ya kamata shugaban Najeriya ya kai zuwa Gambiya a karkashin kungiyar Ecowas an tura ta gaba zuwa juma'a.

kungiyar ta ecowas dai ta yanke  shwarar aikewa da tawaga zuwa kasar Gambiya domin yin matsin lamba ga shugaba Yahya Jammeh da ya sauka daga kan mukaminsa.

A gefe daya kotun kolin kasar ta Gambiya tana shirin bude bincike akan zaben da aka gudanar a kasar bisa bukatar shugaban kasar.

Yahya Jammeh ya yi amai ya lashe akan sakamakon zaben kasar, abinda ya jawo masa suka daga kasashen duniya.

Jan 11, 2017 19:11 UTC
Ra'ayi