• Cote De Voire: An Kafa Sabuwar Gwamnati mai ministoci kadan

Cote De Voire: An Rage Yawan Ministoci Daga 35 Zuwa 28.

Kamfanin dillancin labarun Reuters  ya nakalto cewa bayan da  shugaban kasar cote De Voire Alassan Outtara ya karbi murabus din pira minista Daniel Kablan Duncan, an rage yawan ministocin kasar daga 35 zuwa 28.

Tun a ranar talata ne dai shugaban na Cote De Voire  ya nada daya daga cikin mashawartansa a jam'iyyar da ta ke mulkin kasar, Amadu Gon kolibali a matsayin sabon Pira ministan kasar.

Bugu da kari, shugaban kasar ta Cote De Voire ya ayyan Janar Seiko Turi a matsayin sabon kwamandan sojojin kasa, sai kuma Jamar Nikola Kuadio a matsayin kwamandan rundunar Gendarmeri. Sai kuma Yusuf Koyati wanda aka nada a matsayin shugaban yan sandar kasar.

Sauyin gwamnatin kasar ya zo ne a lokacin da sojojin kasar su ke bore saboda karancin albashi da kuma neman a kara musu makami.

Jan 11, 2017 19:11 UTC
Ra'ayi