Magoya bayan harkar musluncia Najeriya sun gudanar da jerin gwano a birnin Abuja domin neman a saki sheikh Ibrahim Zakzaky.

Wannan matakin dai ya zo bayan shudewar wa'adin da kotun tarayya ta bayar ga gwamnati na a saki Malamin a cikin 45 tare da mai dakinsa ba tare da wani sharadi ba, inda suke kira ga gwamnati da mutunta doka.

Sun kuma gudanar da gangamia  gaban ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta Najeriya, tarte da mika mata korafinsu na neman a saki malamin nasu.

Ita ma a nata bangaren kungiyar Amnesty Int. ta kirayi gwamnatin tarayyar najeriya da ta mutunta doka ta bi umarin kotun tarayya da ta yi umarnin a saki shekh Zakzaky.

Dan rahotonmu a Abuja Dauke karin bayani.

Jan 17, 2017 19:25 UTC
Ra'ayi