Mar 28, 2017 17:17 UTC
  • Afrika Ta Kudu : Ana Juyayin Rasuwar Ahmed Kathrada

Al'ummar Afrika ta kudu na juyayin rasuwar daya daga cikin shugabannin yaki da mulkin wariyar launin fata na kasar Ahmed Kathrada wanda Allah ya yiwa rasuwa yana da shekaru 87 a duniya.

A farkon watan nan ne aka kwantar da Kathrada a asibitin Donald Gordon don yi masa tiyata a kwakwaluwa, kuma ya rasu ne a wannan Talata kamar yadda cibiyar dake kula da al'amuransa ta sanar.  

Kathrada na daga cikin wadanda aka daure a shekarar 1964 tare da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela, sakamakon samunsu da  laifin yunkurin kifar da gwamnatin farar fata mai mulkin nuna wariya.

Kathrada wanda ake kira da "Oncle Kathy" ya kwashe shekaru 26 da watanni 3 a daure, kuma ya yi shekaru 18 a mumunan gidan yarin Robben Island, kuma bayan kawo karshen mulkin wariya, Kathrada ya taba zama mai ma Mandela shawara kan harkokin majalisa daga shekarar 1994 zuwa 1999. 

Marigayin, wanda Musulmi ne, ya yi fice wurin goyon bayan fafutikar kafa kasar Palasdinu. 

Tags

Ra'ayi