Mayu 25, 2017 18:09 UTC
  • 'Yan Sandan Kenya 5 Sun Mutu Sakamakon Harin 'Yan Ta'addan Al-Shabab

Rahotanni daga kasar Kenya sun bayyana cewar wasu 'yan sandan kasar su biyar sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta al-Shaba na kasar Somaliya suka kai musu kusa da kan iyakan kasar Kenyan da Somaliya.

Kafafen watsa  labarai sun jiyo babban jami'in 'soja mai kula da hare-haren da ake kai wa 'yan ta'addan Al-Shabab  a arewa maso gabashin kasar Kenyan  Mohamud Ali Saleh yana fadin cewa 'yan ta'addan sun kai wa jami'an sandan hari ne a hanyarsu ta zuwa yankin a shirin da ake yi na karfafa dakarun da suke fada da 'yan Al-Shabab din inda suka kashe biyar daga cikinsu.

Wasu majiyoyin sun ce 'yan ta'addan sun kai harin ne da ababe masu fashewa a kan motar da take dauke da jami'an 'yan sandan inda suka tarwatsa motar.

Wannan harin dai ya zo ne kwana guda bayan da wasu 'yan sandan su 8 suka rasa rayukansu sakamakon irin wannan harin da aka kai wa jami'an 'yan sandan sau biyu. Kungiyar Al-Shabab din dai ta dauki alhakin kai wadannan hare-haren.

 

Tags

Ra'ayi