• Gwamnatin Niger Ta Bada Sanarwan Fara Wani Sabon Shiri Na Yaki Da Ta'addanci

Gwamnatin jumhuriyar Niger ta bada sanarwan fara wani sabon farmki kan yan ta'adda a yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wata majiya wacce bai bayyana sunata ba na cewa, gwamnatin jumhuriyar Niger ta fara wani farmaki kan yan ta'adda a lardin Tillaberi daga yammacin kasar.

Majiyar ta kara da cewa sojojin kasar 245 ne suka fara wannan farmakin don maganci ayyukan ta'addanci wadanda yan ta'adda masu  shigowa daga daga kasar Mali suke haddasawa a cikin kasar.

A cikin yan watannin da suka gabata dai ana samun yan ta'adda wadanda suke shigar jumhuriyar ta Niger daga kasar Mali suna kisan jami'an tsaron kasar musamman wadanda suke aiki a kan iyakokin kasashen biyu.

Banda haka gwamnatin  Niger tana yakar yan ta'adda na kungiyar Boko Haram a yankin Diffa daga gabacin kasar tun fiye da shekaru ukku da suka gabata.

Jun 17, 2017 19:14 UTC
Ra'ayi