• Shugaban Kasar Masar Ya Bukaci A Dorawa Kasar Turkiya Takunkumi Irin Na Qatar

Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Sisi ya bukaci kasashen duniya su dorawa gwamnatin kasar Turkiya takunkumi har zuwa lokacin da zata daina goyon bayan kasar Qatar.

Shafin labarai na yanar gizo, daga kasar Britaniya mai suna "Midle  East Monitotor" ya nakalto shugaban Abdul-Fatah Sisi na kasar Masar yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da Sarkin kasar Bahrain Ham bin Isa Ali-Khalifa a ranar Alhamis da ta gabata. 
shugaban ya bukaci a dorawa Turkiya takunkumi ne don goyon bayan da take bawa kasar Qatar kan killaceta da wasu kasashe 7 suka yi.

Har'ila yau Abdul-Fatah Sisi yana zagrin shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyeeb Ordugan da goyon bayan Ikhwan Al-Muslimin na kasar ta Masar.

Turkiya wacce saudia take son ta zama 'yar amshin shatan ta, ta yi suka ga kasashen larabawa da suka kauracewa kasar Qatar kan zargin goyon bayan yan'ta'adda a yankin, ta kuma bukaci wadan nan kasashen su kawo karshen killacewar da gaggawa.

Jun 17, 2017 19:15 UTC
Ra'ayi