• Mutane Da Dama Ne ake Zaton Sun Mutu Sanadiyyar Hari kan Wani Kauye A Taraba

Mutane da dama ne ake zaton sun rasa rayukansu, a lokacin da aka kai hari kan wani kauyen Fulani makiyaya a jihar Taraba.

 

Jaridar Daily Trust ta nakalto wani mai suna Malam Bello Haruna yana cewa wasu matasa yan kabilar Mambilla ne suka kai hari kan kauyensu suka kona gidaje da dama suka kuma kashe dabbobinsu, amma shi da matarsa da kuma yayansa biyu sun tsira da ransu.

Majiyar yansanda ta jihar taraba ta bayyanawa Daily Trust kan cewa har yanzun basu da labarin ko akwai wanda ya rasa ransa, amma jami'an tsaro sun kawo karshen rikicin.

Wani daga garin Ngorije mai suna Malam Ibrahim dauda ya fadawa dan rahoton daily Trust kan cewa wadannan matasa sun so su kai irin wadannan hare hare a garinsu amma jami'an tsaron da suka zo aa kani lokacin sun hana hakan faruwa, da wannan dalilin ne suka kai hare haren a kauyukan yankin.

 

Jun 19, 2017 06:51 UTC
Ra'ayi