• Tarayyar Afirka Ta Nuna Damuwa Akan Karuwar Rikicin Kan Iyakokin Kasashen Djibouti Da Eritrea

Bayan ficewar sojojin kasar Katar daga kan iyakokin Djibouti da Eritrea,kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana damuwarta akan karuwar zaman dardar tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato shugaban cibiyar tarayyar Afirkan Musa Faki Muhammad yana bayyana damuwarsa akan yadda kasashen biyu su ke kai ruwa rana a tsakanin kasashen Eritrea da Djibouti, tun bayan da kasar Katar ta janye sojojinta na zaman lafiya.

Kasar ta Katar ta yanke hukuncin janye sojojin nata ne, bayan da kasar Djibouti ta marawa Saudiyya baya a rikicin kasashen larabawan yankin tekun pasha.

Rikici iyaka tsakanin kasashen biyu ya fara ne tun a 2008 bayan da sojojin Eritirea su ka mamaye wani tsauni da ya ke a matsayin mashigar tekun read sea, arewacin babban birnin Djobouti.

Kasar Djibouti ta marawa kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Masar da su ka yanke alakar diplomasiyya da Katar a ranar 5 ga watan Yuni.

Jun 19, 2017 10:57 UTC
Ra'ayi