• Kofi Anan Ya yi Gargadi Akan Makomar Kasar Demokradiyyar Congo

Tsohon babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan da wasu tsoffin shugabannin Afirka sun yi gargadi akan hatsarin da ya ke fuskantar makomar kasar Demokradiyyar Congo

Tsohon babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan da wasu tsoffin shugabannin Afirka sun yi gargadi akan hatsarin da ya ke fuskantar makomar kasar Demokradiyyar Congo.

A wani bayani na hadin gwiwa wanda Kofi Anan da tsoffin shugabannin kasashen Najeriya, Olushegun Obasanjo, da Boni Yaya na Benin, da Thabo Mbeki na Afirka ta kudu, su ka fitar, sun bukaci da a yi amfani da hanyoyin sulhu da zaman lafiya domin warware rikicin kasar.

Bugu da kari, bayanin ya kunshi yin kira da a gaggauta yin manyan zabuka a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Tun bayan dage lokacin da ya kamata a yi zaben shugaban kasa a 2016 a kasar ne aka shiga dambaruwar siyasa, wanda ya kai ga yin Zanga-zangar da ta juye zuwa tarzoma da kashe mutane da dama.

 

 

Jun 19, 2017 11:59 UTC
Ra'ayi