• Mali: An Kashe Wasu Mahara Hudu A Kusa Da Birnin Bamako

Ministan Tsaron kasar Mali ya sanar a jiya lahadi da dare cewa; An kai wa wurin shakatawa na Kangaba hari, tare da yin garkuwa da mutanen da ke cikinsa.

Ministan Tsaron kasar Mali ya sanar a jiya lahadi da dare cewa; An kai wa wurin shakatawa na Kangaba hari, tare da yin garkuwa da mutanen da ke cikinsa.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato Ministan tsaron na kasar Mali,Salyf Traore yana ci gaba da cewa; Sojojin kasar da hadin gwiwar sojojin Majalisar Dinkin Duniya sun shiga cikin ginin na  Kangaba tare da kwato mutane 20 da aka yi garkuwa da su, sannan kuma aka kashe maharan su hudu.

Wata majiyar labaru daga kasar ta Mali ta ce; a yayin harin an kashe wani mai yawon bude ido dan kasar Faransa da kuma jikkata 'yan sanda takwas.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai harin.

Jun 19, 2017 12:00 UTC
Ra'ayi