• An Fara Gudanar Da Wasu Shirye-Shirye Na Ranar Quds A Senegal

An fara gudanar da wasu shirye-shirye na ranar Quds a kasar Senegal, da suka hada da tarukan karawa juna sani da sauransu.

Cibiyar yada al'adun muslunci ta sanar da cewa, wadannan taruka ana gudanar da su bisa take Palastinu a mahangar addinai da aka safkar daga sama, wanda karamin ofishin jakadancin Iran da kuma Jami'ar Almustafa suke daukar nauyin gudanar su.

Tarukan suna samun halartar malamai da kuma masana gami da 'yan siyasa dama sauran jama'ar gari, inda ake gabatar da bayanai a kan matsayin Palastinu a tarihin addinai, da kuma masallacin quds wanda ke da matsayi na musamman a cikin dukkanin addinai da Allah ya safkar.

Baya ga haka kuma ana gudanar da gasar kur'ani a bangare guda duk a karkashin wanann shiri, inda a ranar Juma'a kuma za a gudanar da babban taro na ranar Quds ta duniya.

 

 

Jun 19, 2017 17:24 UTC
Ra'ayi