Jun 28, 2017 06:29 UTC
  • Sojin Libiya Sun Fara Kai Farmakin Tsarkake Birnin Bangazi

Dakarun Tsaron Libiya Sun Fara kai farmaki daga Kusurwowi guda hudu na yankin Assabiri dake a matsayin tungar karshe na masu dauke da makamai a birnin Bangazi dake arewa maso gabashin kasar

Kafafen yada Labaran Larabawa sun nakalto Kanar Ahmad Mismari daya daga cikin manyan jami'an tsaron kasar Libiya na cewa a wannan Talata Sojojin kasar dauke da manyan makamai sun killace yankin Assabiri dake a matsayin tungar karshe na masu dauke da makamai a birnin na Bangazi.

Ahmad Mismari ya kara da cewa ganin mahiman da wannan yanki ke da shi, da kuma yadda aka dasa nakiyoyi a yankin, tsarkakke shi zai dauki lokaci, kuma ya zuwa yanzu, Sojojin kasar sun tone nakiyoyi dubu uku da dari takwas.

Kimanin wattani uku da suka gabata ne, Dakarun tsaron Libiyan  karkashin jagorancin Khalifa Haftar suka bayyana shirin su na tsakake yankunan Assabiri da Sukul-Huth dake birnin Bagazi.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Dakarun kasar ta Libiya suka samu nasarar shiga yasnkin Sukul-Huth tare da tsarkake shi daga 'yan ta'adda.

Tags

Ra'ayi