Jul 10, 2017 19:07 UTC
  •  Tawagar Majalisar Dokokin Jamhuiryar Nijar Na Ziyara A Iran

Shugaban kwamitin kawance a tsakanin majalisun Iran da Nijar ya ce; Aiki tare a tsakanin kasashen musulmi zai sa su yin tasiri a fagen siyasar kasa da kasa.

Shugaban kwamitin kawance a tsakanin majalisun Iran da Nijar ya ce; Aiki tare a tsakanin kasashen musulmi zai sa su yin tasiri a fagen siyasar kasa da kasa.

Mahdi Farshad wanda ya gana da  takwarana daga bangaren kasar jamhuriyar Nijar, Massani  Cornei a nan Tehran a yau litinin ya yi ishara da yadda alakar kasashen biyu ta cika shekaru 30 sannan kuma ya kara da cewa:  Kwamitin kawance na kasashen biyu a shirye ya ke domin shafe fagen yin aiki a tsakanin majalisun biyu.

Har ila yau Farshad ya ce kasar Iran za ta yi aiki a tare da Nijar a bangarorin tattalin arziki da kiwon lafiya da kasuwanci.

A nashi gefen, Massani Cornei daga Jamhuriyar Nijar, ya yaba da jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ya ce tana da matsayi a siyasar waje ta kasarsa.

Tags

Ra'ayi