• EFCC: Dukiyar Satar Da Aka Gano A Wajen

Mukaddashin shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya (EFCC), Ibrahim Magu, ya bayyana cewa dukiyar sata da yanzu aka gano daga wajen tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, a matsayin wani abin da bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da abin da ake zargin ta sata.

Mr. Ibrahim Magu ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi ta gidan talabijin din TVC na kasar inda ya ce: Abin da ya zuwa yanzu muka kwato daga wajen Diezani, ba a bakin komai yake ba, hakan wani so man tabi ne kawai, yana mai cewa hukumar tasa tana ci gaba da gano almundahanar da tsohuwar ministar ta yi.

Ya zuwa yanzu dai hukumar EFCC din ta gano da kuma kwato kudaden da suka kai Naira Biliyan 47.2 da kuma wasu kudaden da kadarorin da suka kai Dala Miliyan 487.5 da suke da alaka da tsohuwar ministan man fetur din Mrs. Diezani Alison-Madueke.

Har ila yau kuma wasu hukumomin tsaro a kasashen Amurka da Birtaniya suna bincike tsohuwar ministar kan zargin halalta kudaden haramun, wanda Mr. Magun ya ce hukumar tasa na ci gaba da aiki da wadannan hukumomin wajen ci gaba da gano wasu kudaden da tsohuwar ministar ta yi awun gaba da su.

 

Aug 11, 2017 05:46 UTC
Ra'ayi