• Najeriya Ta Tura Sojoji Zuwa Kasar Liberiya

Majiyar Sojan Najeriya ta ce; Kasar ta tura sojoji 230 zuwa Liberiya a karkashin dakarun tabbatar zaman lafiya na kasa da kasa

Kamfanin dillanci labarai na Xinhua ya ambato babban hafsan hafsoshin kasar Najeriya, Tukur Burutai yana cewa; Tura sojojin yana a karkashin shirin zaman lafiya ne na Majalisar Dinkin Duniya ne.

Burutai wanda ya ke duba horon makwanni hudu da ake bai wa sojojin na zaman lafiya a jahar Kaduna da ke arewacin kasar, ya jaddada cewa; Wajibi ne sojojin su kauce aikata duk wani abu wanda zai zubar da mutunci kasar."

Kasar Najeriya na daga cikin wadanda su ka yi fice wajen aikewa da sojojin zaman lafiya zuwa kasashe daban-daban na duniya. Daga samun 'yancin kasar a 1960 zuwa yanzu Najeriya ta aike da sojoji fiye da 20,000 zuwa kasashe 40 a cikin Afirka da kuma sassa daban-daban na duniya.

 

Aug 11, 2017 11:10 UTC
Ra'ayi