• Kasar Venezuela Ta Maida Martani Ga Barazanar Donald Trump

Ma'aikatun tsaro da na harkokin wajen kasar Venezuela sun yi Allah wadai da barazanar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa kasarsu.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato ma'aikatar tsaron ra Venezuela tana cewa; Kai wa Kasar hari wani nau'i ne na hauka.

Kakakin gwamnatin Venezuela ya sanar da cewa; a halin da ake ciki yanzu ma'aikatar harkokin wajen aksar tana kan shirya martanin da ya dace akan barazanar ta Donald Trump ta kai wa kasar hari.

A daren juma'a ne dai shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya ce; Da akwai matakai da yawa da Amukra za ya dauka akan kasar Venezuela daga ciki hadda na soja.

Aug 12, 2017 09:19 UTC
Ra'ayi