• Kokarin Kasar Tunusiya Na Sake Maida Alakar Jakadanci Da Kasar Siriya

Wata 'yan Majalisar Dokokin Kasar Tunusiya ta yi furuci da cewa: Matsin lambar kasashen waje ne ya hana hanzarta maida alakar jakadanci tsakanin kasashen Tunusiya da Siriya.

Rabihatu bintu Husain 'yan Majalisar Dokokin Kasar Tunusiya ta yi furuci da cewa: Tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan kasar Tunusiya ne ya hana hanzarta sake maida alaka tsakanin kasashen Tunusiya da Siriya, saboda a ziyarar da tawagar kasar Tunusiya ta kai zuwa kasar Siriya bangarorin biyu sun cimma matsaya kan hanzarta maida alaka a tsakanin kasashensu.

Tun a watan Fabrairun shekara ta 2012 ne mahukuntan Tunusiya na wancan lokacin suka bi sahun kasashen Larabawan yankin tekun Pasha wajen yanke alakar jakadancin kasar da Siriya da nufin goyon bayan 'yan tawayen kasar a kokarin da suka yi kawo karshen gwamnatin Bashar Asad.

Aug 12, 2017 12:02 UTC
Ra'ayi