• Yawan Mutanen Da Aka Kashe Tun Bayan Zaben Shugaban Kasa A Kenya Ya Kai 11

Akalla mutane 11 suka rasa rayukansu a kasar Kenya a karawar jami'an tsaro da magoya bayan Raila Odinga tun bayan da aka kammala zaben shugaban kasa a shekaran jiya.

Jaridar Rasha Today ta bayyana cewa tun bayan zaben shugaban kasa a shekaran jiya Alhamis an fara tashe-tashen hankula a wurare da dama a cikin kasar. Masu tada hankalin dai suna nuna rashin amincewar da sakaman zaben na ran Alhamis, suna kuma zargin cewa jam'iyyar shugaban kasa Uhuri Kenyata ta yi masa magudi ne, wanda ya kai shi ga lashe shi.

Hukumar Zaben kasar dai ta bayyana cewa shugaban kasa mai ci Uhuru Kenyata ne ya lashe zaben shugaban kasar tare da samun kashi 55 % na yawan kuri'un da aka kada.    

Aug 12, 2017 17:43 UTC
Ra'ayi