• Hukumar Yaki Da Safarar Mutane: Yan Nigeria 520 Ne Za'a Dawo Da Su Gida Daga Libya A Wannan Wantan

Hukumar yaki da fataucin mutane ta Nigeria NAPTIP ta bayyana cewa yan Nigeria 540 ne za'a dawo dasu gida Nigeria a cikin wannan wata ta Augusta da muke ciki daga kasar Libya.

Jaridar Thisday ta Nigeria ta nakalto hukumar tana fadar haka a jiya jumma'a, ta kuma kara da cewa za'a dawo da su kasarne ta tashar jiragen sama na Murtala Mohammad dake Lagos. 

A wani labarin Diectan hukumar ta yaki da fataucin mutane  Julie Okah-Donli ta bayyana cewa hukumarta ta kubutar da yan Nigeria kimani 12,000 wadanda suka fada hannun masu safarar mutane, kuma ta gurfanar da mutane 325 wadanda ake zargi da safarar mutane a gaban kotuna daban daban.

Banda haka ta ce a cikin mutane 540 da za'a dawo da su gida a cikin wannan watan tuni 180 daga cikinsu sun isa Lagos. Sannan ta ce, daga farkon wannan shekara ta  2017 yan Nigeria 2000 ne aka dawo da su kasar daga kasar Libya kadai.

Daga karshe Ditectan ta bayyana cewa hukumarta tana bukatar kudade karin kudade don kyautata wuraren ajiyar da kuma kula da wadanda suka shiga hannusu na wadanda aka sata da kuma bariyin mutanen. Da kuma lkula da lafiyansu da suturarsu har zuwa lokacinda za'a tsaida yadda za'a yi da su.

 

Aug 12, 2017 17:43 UTC
Ra'ayi