• Yan Tawayen Kasar Sudan Ta Kudu Sun Ce Sun Kwace Iko Da Garin Pagak Daga Sojojin Gwamnati

Majiyar yan tawayen kasar Sudan ta Kudu ta bayyana cewa, dakarunsu sun dawo da ikonsu kan garin Pagak daga hannun sojojin gwamnati kwana guda bayan sun koresu daga garin.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Lam Paul Gabriel kakakin yan tawayen yana fadar haka a safiyar yau Asabar, ya kuma kara da cewa kafin hakan, garin Pagak shi ne babban sansanin dakarun yan tawayen a kusa da kan iyaka da kasar Ethiopia. Kuma kwanaki biyar da suka gabata ne sojojin gwamnati suka kwace iko da shi amma sun sami nasarar dawo da ikonsu a garin a safiyar yau Asabar..

Amma Dickson Gatluak Jock, kakakin mataimakin shugaban kasar ta Sudan ta Kudu ya musanta cewa garin Pagak ta kubuce masu, amma ya tabbatar da cewa an fafata da mayakan yan tawaye kuma sun rasa sojojin ukku a fafatawar.

Mataimakin shugaban kasar Taban Deng Gai, tsohon dan tawaye ne wanda ya koma bangaren gwamnati a shekarar da ta gabata, sannan aka bashi mukamin mataimakin shugaban kasa, a halin yanzu sojojinsa masu biyayya ga gwamnatin kasar suna suke fafatawa da yan tawaye a garin na Pagak. 

Garin Pagak yana da muhimmanci ga yan tawayen don ta nan ne suke satar shiga da makamai daga kasashen waje. An fara yakin basasa a kasar ta Sudan ta kudu ne cikin watan Decemban shekara ta 2015, bayan da shugaba Silva-Kiir ya kori mataimakinsa Riek Machar. Kuma tun watan Decemban shekarar da ta gabata ne shuwagabannin Afrika suka bukaci a yiwa Riek Marcha durin talala a kasar Afrika a kokarin da suke yi na kawo karshen yakin.

 

Aug 12, 2017 17:44 UTC
Ra'ayi