• An Kama Wani Dan Yawon Shakatawa Dan Kasar Italia Tare Da Zarkin Kashe Ma'aikacin Wani Hotel A Masar

Majiyar ma'aikatar sharia ta kasar Masar ta bayyana cewa tana tsare da wani dan yawaon shakatawa dan kasar Italia tare da zarginsa da kisan wani mai kula da Hotel a bakin ruwa na Marsa Alam.

Kamfanin dillancin Labaran reuters ma'aikacin mai kula da aikin ginin wata Hotel a bakin teku na Marsa Alam ya yi cacan baki da dan Italia a ranar Alhamis, inda ya hana shi shiga wasu wurare a yankin kafin a sami labarin mutuwarsa.

Ministam yawon shakatawa na kasar Masar ya tabbatar da wannan labarin a jiya jumma'a ya kuma kara da cewa dan kasar ta Italia mai suna Ivan Pascal Moro ya tabbatar da cewa yana da hannun wajen mutuwar ma'aikacin Hotel din. A halin yanzu dai ana tsare da Ivan Pascal Moro na wani mako guda kafin ya gurfana a gaban kotu. 

Ministan ya kara da cewa akwai wasu yare tare da mutumin wadanda shekarunsu ya kama daga 6 zuwa 15, kuma suka shaida cacanbakin da yayi da ma'aikacin, sannan bayan tsare shi suna karkashin kula na Hotel din kafin zuwa wani jami'an ma'aikatar yawon shakaratawa na kasar Italia don ya maidasu gida.

 

Aug 12, 2017 17:44 UTC
Ra'ayi