• Gwamnatin Kasar Libya Ta Bukaci Kudade Daga Tarayyar Turai Don Yaki Da Kwararar Baki

Babban komandan rundunar sojojin kasar Libya Janar Halifa Haftar ya yi kira ga tarayyar Turai da ta ware kasasfin kudi mai yawa don yaki da kwararan bakin haure zuwa nahiyar daga kasar Libya.

Halifa Haftar ya fadawa jaridar kasar Itakiya mai suna "Corriere della Sera" cewa dole ne kasashen turai su ware kudade kimani dalar Amurka billion 20 a cikin shekaru 20 zuwa 25 masu zuwa don dakatar da kwararar bakin haure daga kudancin kasar libya zuwa kasashensu.

Haftar ya kara da cewa, a ganawarsu da Shugaban kasar Faransa Manuel Macron a kwanakin baya, ya bukaci rundunar sojojin kasar ta Libya ta aiko da jerin bukatunta don ganin an kawo karshen kwarar bakin haure zuwa kasashen turan daga Libya. Ya ce tuna an aikata mata bukatun su, wadanda suka hada da   motoci masu sulke, jeragen sama masu leken asiri, jiragen masu saukar ungulu, da tabarau wadanda ake iya kallo da su cikin dare da sauransu. 

Har'ila yau Halifa Haftar ya soki Fa'iz Surar Priministan rikon korya na kasar da rashin neman shawararsa kafin ya bawa sojojin ruwan kasar Italia izinin shiga ruwan kasar libya.

Majalisar dokokin kasar Italia tare da amincewar Fa'iz Suraj Priministan Kasar Libya ta amincewa sojojin ruwan kasar ta su shiga gabatar tekun medeteranian na kasar libya don hana bakin haure zuwa tarayyar Turai, amma ba tare da sun tuntubi Halifa Haftar ba, wannan ya hana sojojin Italiyan zuwa kusa da kasar.

Aug 12, 2017 17:45 UTC
Ra'ayi