Sep 10, 2017 14:47 UTC
  • Shuwagabannin Afrika Sun Yi Suka Kan Irin Shishigin Da Kasashen Waje Suke Yi A Harkokin Libya

Shuwagabannin kasashen Afrika sun yi suka kan yadda wasu kasashen duniya suke tsoma baki a cikin harkokin kasar Libya, inda suke zargin cewa tsoma bakin nasu ne ya hana tabbatar da zaman lafiya a kasar

Majiyar muryar JMI ta nakalto Musa Faki Mohammad babban skataren kungiyar tarayyar Afrika yana fadar haka a jiya Asabar a lokacinda yake bude taron komitin kungiyar na musamman dangane da rikicin kasar ta Libya, ya kuma yi kira da bangarorin yan siyasa na kasar Libya da su hade kansu don rufe damar da kasashen waje suke da shi na tsoma bakin cikin harkokin cikin kasar.

Shugaban kasar Congo Brazaville Denis saso Ngesu wanda yake cikin komitin na tarayyar Afrika don warware rikicin kasar ta Libya ya ce kungiyar tarayyar Afrika bata da wata manufa ta boye dangane da rikicin da ke faruwa a kasar ta Libya don haka yayi kira da shuwagabannin yan siyasa a kasar su hada kansu don kawo karshen matsalolin kasar ta hanyar tattaunawa. 

Sai kuma Gassan Salama wakilin MDD dangane da rikicin na kasar Libya ya bayyana cewa shishigin da kasashen duniya suke yi a cikin harkokin kasar Libya yana hana ruwa gudu a kokarin da suke na kawo karshen rikicin, don haka ya yi kira ga kasashen da suke shishigi a cikin lamuran kasar da su kyale MDD kadai ta shiga tsakani don warware rikincin wannan kasar.

Tags

Ra'ayi