• An Dage Taron Afrika Da H.K Isra'ila

Ma'aikatar harkokin wajen H.K Isra'ila, ta ce bisa bukatar shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé, an dage taron koli da kasar za ta yi da kasashen Afirka.

Tun da farko dai an tsara za'a gudanar da taron na tsakanin Isra'ila da wasu kasashen Afrika 54 daga ranar 23 zuwa 27 na watan Oktoba mai zuwa a birnin Lome na kasar Togo.

Sanarwar da ma'akatar ta fitar a jiya, ta yi nuni da cewa, domin tabbatar da gudanar taron cikin nasara, kasar Togo tana bukatar gudanar da karin shirye-shirye, sai dai kuma, sanarwar ba ta bayyana yaushe za a gudanar da taron ba.

Wasu kafofin yada labarai a Togo sun ce watakila an soke gudanar da taron ne bisa la'akari da kin amincewa da shi da kasar Palesdinu da wasu kasashen Afirka su ka yi.

Don kyautata dangantakar dake tsakanin Isra'ila da kasashen Afirka, Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya taba kai ziyara kasashen Rwanda da Kenya da Uganda da Habasha da sauran wasu kasashen Afirka a shekarar 2016, kana ya halarci taron koli na kungiyar ECOWAS da aka gudanar a kasar Liberia a watan Yunin da ya gabata, saidai a nan ma wasu kasashen Afrika sun cacaki gayyatar da aka ma Netanyahu inda suka rage karfin wakilcinsu a taron.

Sep 12, 2017 05:49 UTC
Ra'ayi