• Marocco Ta Bukaci Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Kawo Karshen Ta'addancin Isra'ila

Ministan harakokin wajen Maracco ya ce ya zama wajibi kungiyoyin kasa da kasa su kawo karshen ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila ke aiwatarwa a kan al'ummar Palastinu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Nasse Bourita ministan harakokin wajen kasar marocco a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da ya gudana jiya talata a birnin Alkahira na cewa; lokaci yayi da kungiyoyin kasa da kasa za su shiga cikin matsalar palastinu domin kawo karshen ta'addancin da HKI ke aiwatarwa a kan al'ummar Palastinu.

Yayin da yake bayyani game da jinkiri wajen magance matsalar Palastinu da kuma rikcin kasashen Siriya, Yemen, Libiya da Iraki, ministan ya ce hakan zai mummunan tasiri game da makomar al'ummar kasashen, sannan kuma ya ce idan kasashen musulmi za su hada kansu za su iya magance matsalar Palastinu da rikicin yankin.

A yayin da ya koma kan kasar Iraki, Nasse Bourita ya jinjinawa gwamnatin kasar kan yadda ta yaki 'yan ta'adda, sannan ya bayyana goyon bayansa kan hadin kan al'ummar kasar.

Sep 13, 2017 08:30 UTC
Ra'ayi