• Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Birnin Tripoli Fadar Mulkin Kasar Libiya

Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka yi awungaba da wani likita.

Kafofin watsa labaran Libiya a jiya Talata sun watsa labarin cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya tare da sace wani likita.

Har yanzu babu wata kungiya ko jama'a da suka dauki alhakin sace likitan. Tun bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011 aka samu bullar kungiyoyi masu dauke da makamai da suke sace mutane suna neman kudin fansa daga iyalansu lamarin da ya kara wurga al'ummar kasar cikin masifar rashin tsaro.  

Sep 13, 2017 12:19 UTC
Ra'ayi