• Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ya Kira Yi Kasar Myanmar Da Ta Dakatar Da Kai Wa  Rohingya Hari.

A yau laraba ne babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya bayyana cewa an yi wa muslmin Rohingya kisan kiyashi a kasar Myanmar, tare da yin kira da a kawo karshen hakan.

Guterres ya ce; "Ina yin kira ga mahukuntan kasar Myanmar da su kawo karshen harin soja da kuma dawo da aiki da doka."

Da ya ke amsa tambyar 'yan jarida akan ko ya yarda an yi wa musulmin Rohingya kisan kiyashi, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya bayyana cewa:

"Tunda kaso daya bisa uku na al'ummar Rohingya sun fice daga cikin kasar, wace kalwa tafe dacewa ka yi amfani da ita domin bayyana halin da su ke ita?

Fiye da mutane 380,000 yan kabilar Rohingya suka tsallaka iyaka zuwa kasar Bangladesh domin tserewa kisa a kasarsu.

Sep 13, 2017 19:03 UTC
Ra'ayi