• Najeriya: An Sa Dokar Ta Baci A Jahar Abia

Gwamnatin Jahar Abia ta sanar da kafa dokar ta bacin ne ta kwanaki biyu wacce za ta fara daga gobe alhamis.

Gwamnan Jahar ta Abia Okezie Ikpeazu wanda ya fitar da bayani akan dalilin kafa dokar, ya yi ishara da rikicin da aka samu a tsakanin wasu kungiyoyi musamman masu rajin kafa kasr Biafar ta (IPOB), da kuma sojojin Nigerian Army.

Har ila yau, gwamna Ikpeazu ya ce; Gwamnatin tana kuma sane da fara farmakin da sojoji suka yi a yankin na kudu maso gabas, mai taken Rawar kasa na 2, wanda manufarsa ita ce fada da masu garkuwa da mutane, kisan gilla da kuma ayyukan masu son ballewa daga Najeriya.

Gwamnan ya kuma ce; Jahar Abia tana cikin jahohin tarayyar Najeriya, kuma ta yi imani da fifikon tsarin mulkin Najeriya bisa da kowace irin doka.

 

 

 

Sep 13, 2017 19:05 UTC
Ra'ayi