• Kamaru: Harin Kunar Bakin Wake Na Boko Haram  Ya Kashe Fararen Hula 4

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya amabto majiyar tsaron kasar ta Kamaru tana cewa; Wata buduruwa ce ta kai harin a kusa da masallacin Sandawadjiri da kusa da iyakar Najeriya.

Majiyar ta kara da cewa; Baya ga fararen hula 4 da suka kwanta dama, ita kanta wacce ta kai harin ta halaka.

Hare-hare irin wadannan dai  ana danganta su ne da kungiyar boko haram.

Arewacin kasar Kamaru  wanda yake da iyaka da Najeriya da kuma  kasar chadi yana da yankunan da kungiyar ta boko haram take tsananta kai hare-hare.

A bisa rahoton Majalisar Dinkin Duniya Kamaru ce kasa ta biyu bayan Najeriya da kungiyar ta boko hari take tsananta kai wa hari.

Sep 13, 2017 19:06 UTC
Ra'ayi