• Miliyoyin Yara Suna Cikin Barazanar Kamuwa Da Cutar Kyanda Sanadiyyar Rashin Biyan Kudaden Riga Kafi

Ma'aikatar kiwon lafiya a tarayyar Nigeria ta bada sanrwar cewa duk jihohin da basu bada kudaden da yakamata su bayar na allurar riga kafin cutar Kyanda zuwa gobe juma'a ba ba za'a yiwa yara a jihohin allurar riga kafin ba.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto Daraktan hukumar lafiya a matakin farko, wato  the National Primary Health Care Development Agency (NPHCDA) a takaice Faizal Shuaib tana fadara haka a ranar Litinin da ta gabata. Sannan ta kara da cewa jihohi hudu ne kacal suka bada kasonsu na kudaden da ya kamata su bayar na wannan aikin. Kuma sune Jihohin  Kebbi, Borno, Imo da Nasarawa, sannan akwai wasu guda takwas wadanda suka amince da a bayar da kudaden amma basu shigo ba jihohin sun hada da Edo, Kaduna, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Niger and Zamfara. Sauran jihohi 25 da kuma Abuja basu bada komai ba. 

Faiza ta ce Jihar Kano ta bada wani kaso na kudaden wato miliyon 9 cikin million 50 da yakamata ta bayar. Za'a fara aikin allurar riga kafin cutar kyanda wa yara yan kasa da shekaru 5 a ranar 26 ga watan Oktoba mai kamawa.

 

Sep 14, 2017 05:28 UTC
Ra'ayi