• Gwamnatin Masar Ta Fara Karbar Jiragen Yakin Da Ta Saya Daga Rasha

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Rasha ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta fara mikawa kasar Masar jiragen yaki samfurin MIG-29 guda 50 da ta saya daga wajenta.

Kamfanin dillancin Labaran Intertasa na kasar Rasha ya nakalto Vladimir Koojeen mataimakin shugaban kasa kan harkokin tsaro yana fadar haka a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa mikawa kasar Masar dukkan jiragen yaki samfurin MIG- 29 zai dauki shekaru ana yi, ya kuma ce gwamnatin kasar Rasha tana kan alkawarinta na saidawa kasar Masar wadannan jiragen yaki.

Gwamnatin tsohuwar Tarayyae Soviet ce ta fara samar da jiragen yaki samfurin Meek 29 a shekara 1970 sannan a shekara ta 1983 sojojin tarayyar suka fara amfani da su. Kuma har yanzun sojojin Rasha suna amfani da jiragen, har'ila yau tana saida su ga kasashen waje.

Sep 14, 2017 05:29 UTC
Ra'ayi