• Majalisar Kasar Tunisia Ta Amince Da Dokar Kare Tsoffin Barayin Gwamnati

Majalisar dokokin kasar Tunisia ta amince da dokar kare tsoffin jami'an gwamnati wadanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa bayan cacaraki na watanni da dama kan dokar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto labarin daga shafin yanar gizo na Labarai mai suna -تونس الآن- yana cewa dokar wacce ake kira "Fahintar juna kan matsalolin jagoranci" ta bai wa tsoffin jami'an gwamnati da kuma tsoffin sojojin kasar kariya daga gurfana a gaban kotu kan dukiyoyi da ake zargi na jama'a ne suka sata.

Labarin ya kara da cewa 'yan majalisa 117 ne suka amince da dokar, dan majalisa daya kuma ya ki kada kuri'arsa,   yayin da wasu 9 suka ki amincewa, amma yan majalisar wadanda suke adawa da dokar sun fice daga cikin Majalisar suna ta rera taken cewa "mun cika alkawarimmu da kare jinin shahidai". 

Wannan dokar dai ta sanya rigar kariya ga tsoffin jami'an gwamnati na tsohon shugaban kasar Zainul-abideena bin Ali daga bin kadun dukiyoyin da suka mallaka. Majalisar tana ganin kafa dokar zai bawa tsoffin jami'an gwamnatin zasu fito da dukiyoyinsu don zuba jari a harkokin tattalin arzikin kasar ba tare da tsangwama ba.

Shugaban kasar ta Tunisia Al-baji Ka'ed Alsibsi wanda yake daga cikin masu goyon bayan wannan dokar, ya fara gabatar da ita a gaban majalisar dokokin kasar ne shekaru biyu da suka gabata, amma da yaga masu adawa da ita suna da yawa a lokacin sai ya janye ta. 

Sep 14, 2017 05:30 UTC
Ra'ayi