• Ran Gadin Shugaban Kasar Mali A Yankin Sahel Kan Yaki Da Ta'addanci

A ziyara da ya kai kasashen Nijar da Chadi shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ya jaddada wajabcin kafa rundinar hadin gwiwa ta kasashen yankin Sahel don yaki da ta'addanci.

Bayan da ya ziyarci kasar Chadi, shugaba IBK ya isa a birnin Yamai na jamhuriya Nijar inda ya gana da takwaransa Mahamadu Isufu a wannan ziyara da babbab jigonta shi ne hada karfi da karfe don cimma guri guda na yaki da ta'addanci dake barazawa yankin na Sahel.

Ammam babban abunda bangarorin biyu suka fi maida hankali shi ne yadda za'a hada kan kasashen yankin domin kafa rundinar hadin gwiwa ta kasashen na G5 Sahel don yaki da ta'addanci da safara miyagun kwayoyi da bil adama.

Rundinar ta G5 da kasashen da suka hada da Mauritania, Mali, Nijar, Chadi da Burkina faso suka kirkiro ta, babban aikinta shi ne tunkarar duk wata barazana da kuma shawo kan harehare ta'addanci da mayakan dake ikirari da sunan addini ke kaiwa musamen a kasar Mali da makoftanta.

Shugaba Keita a fada a ganawa da takwaransa na NIjar cewa, a matsayin na shugaban wata kasa da muke fama da matsala guda ta ta'addanci muna masu jaddada bukatar hada karfi da karfe don yakar wannan matsala ta hanyar kafa rundinar hadin gwiwa.

Shi kuwa a nasa bangare shugaba Mahamadu Isufu na Nijar ya bayyana cewa muna fama da matsala guda, don haka ne muna yunkuri annniyar hada karfi da duk halin da muke dashi don murkushe wannan matsala dake neman ruguza kasashenmu.

A ranar 9 ga watan nan da muke ciki ne shugaba Ibrahim Bubakar Keita ya kaddamar da ofishin da zai jagoranci ayyukan rundinar.

An dai kaddamar da offishin ne a yankin Sevare dake tsakiyar kasar Mali, inda kuma shugaba Keita ya gana da babban kwamandan kungiyar wanda janar din soji ne na kasar ta Mali da mukadashinsa dan asalin Burkina faso sai kuma babban hafsan soji rundinar na Jamhuriya NIjar.

Shi dai wannan ofishin zai jagoranci ayyukan soji na rundinar ta G5 Sahel data kunshi kasashen biyar.

Rundinar da ake sa ran zata fara aiki kafin karshen wannan wata zata kunshi dakaru 5,000 domin yaki da ta'addanci da safara miyagun kwayoyi da bil adama a yankin na Sahel.

Kasar Nijar dai ta jima da aike sojojinta a kasar Mali da nufin yaki da masu tada kayar baya, inda take da sojoji a cikin tawagar MISMA, sannan kuma tana da sojoji a cikin tawagar wazar da zaman lafiya ta MDD a Mali cewa da MINUSMA.

Kasashen Nijar da Mali dai sun raba iyaka mai tsawon kilomita 400, kuma al'ummar kasashen biyu na magana da wasu yare iri daya da suka da Buzanci, fulatanci.

Bayan kasashen Chadi da Nijar, ana sa ran nan gaba shugaban kasar ta Mali zai isa birnin Ouagadugu na Burkina Faso, inda cen din ma zai gana da takwaransa kan batun na yaki da ta'addanci.

Sep 14, 2017 05:54 UTC
Ra'ayi