Sep 21, 2017 12:41 UTC
  • Sojojin Libya Sun Kwace Garin Sabratah Daga Hannun Masu Dauke Da Makamai

Sojojin kasar ta Libya sun kori kungiyar mai alaka da Da'esh a garin Sabratah da ke yammacin kasar.

Tashar telbijin din Sky News ta larabci ta bada labarin cewa, sojojin Libyan sun dakile duk wani kokari na kungiyar ta Da'esh na kama tsakiyar birnin.

Tun a ranar lahadin da ta gabata ne dai tsakiyar birnin na Sabratah ya zama fagen dagar yaki a tsakanin sojojin na Libya a karkashin Halifa Haftar  da kuma kungiyar ta 'yan ta'adda.

Kasar Libya tana fama da fadace-fadace tun a 2011 da kungiyar tsaro ta Nato ta kifar da gwamnatin Mu'ammar Kaddafi.

 

Tags

Ra'ayi