• Raila Odinga Dan Takarar Gamayyar Jam'iyyun Adawa A Kenya Ya Janye Daga Takara

Shugaban gamayyar jam'iyyun adawa a zaben shugaban kasa wanda za'a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa a kasar Kenya ya bayyana janyewarsa daga takarar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya nakalto Odinga yana fadar haka a wani taron yan jaradi da ya kira a birnin Nairobi a jiya Talata, inda ya kara da cewa janyewarsa daga zaben shugaban kasar mai zuwa zai zama alkhairi ne ga mutanen kasar Kenya da kuma kasashen duniya gaba daya.

Janyewar Odinga tana nuni da cewa yana bukatar a dakatar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu da yakamata a gudanar a ranar 26 na watan da muke ciki, sannan a sanya wata rana don sake zaben.

A ranar daya ga watan Satumban da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasar a kasar ta Kenya, inda sakamakon zaben ya nuna cewa shugaban kasa mai ci Uhuru Kenyata ne ya lashe shi da kashi 55%. Amma Odinga ya ce zaben bai da inganci don akwai kura-kuran da hukumar zaben kasar tayi, da hka kuma ya sami goyon bayan wata ko a kasar wacce ta bata sakamakon zaben sannan hukumar zaben ta sake sanya ranar 26 ga wannan watan don sake zabe.

Oct 11, 2017 06:30 UTC
Ra'ayi