• Gwamnatin Algeria Ta Bukaci A Maida Kasar Syria Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa

Gwamnatin kasar Algeria ta kara jaddada bukatar maida kasar Syria cikin kungiyar kasashen Larabawa.

Jaridar "الشروق" ta kasar Algeria ta nakalto ministan harkokin waje na kasar Abdulqadi Masahel yana fadar haka a jiya Talata . Ministan ya kara da cewa kasar Syria har yanzun tana da kujeranta a cikin kungiyar, sannan ya kara da cewa yakamata kasashen larabawa su sani gwamnatin kasar Syria ta sami nasara a kan yan ta'adda sannan komai ya sauya a kasar.

Masahel ya kammala da cewa ko lokacinda aka dakatar da kasar Syria a cikin kungiyar gwamnatin kasar Algeria bata amince da matakin ba. Ministan harkokin wajen kasar ta Algeria ya yi wannan kiran a cikin watan Satumban da ya gabata.

A ranar 15 ga watan Nuwamban shekara ta 2012 ne kungiyar kasashen Larabawar ta dakatar da kasar Syria daga zama memba a kungiyar tare da zarginta da take hakkin bil'adama.  

Oct 11, 2017 06:31 UTC
Ra'ayi