• Najeriya: Mayakan Boko Haram Da Sojojin Nigeria Sun Yi Musayar Wuta A Garin Gwaza Na Jihar Borno

An yi musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram da kuma sojojin Nigeria a garin Gwaza na jihar Borno a jiya da dare.

Jaridar Daily Trust Ta Nigeria ta nakalto majiyar sojojin kasar tana fadar cewa ta san da batun amma bata yi karin bayani ba. Majiyar ta kara da cewa an dakatar da bude wa juna watar bayan sa'a guda amma har yanzu ba wanda ya san halin da garin yake ciki.

Karin bayani zai zo nan gaba. garin Gwaza dai yana daga cikin garuruwan da Kungiyar ta Boko Haram ta taba mamayewa har ma ta maida shi daya daga cikin manya-manyan cibiyoyin da take iko da su a yankin arewa maso gabacin kasar.

A cikin wannan makon ne aka fara shari'ar mutake kimani dubu 6 wadanda ake tuhuma da hannu cikin ayyukan kungiyar ta boko haram a duk fadin kasar a wuraren da ake tsare da su. Mai yiwuwa wannan yana daga cikin dalilan da kungiyar suka kai harin na jiya a garin Gwaza a mahangar wasu masana.

Oct 11, 2017 06:31 UTC
Ra'ayi