• Nijeriya : Amnesty Ta Damu Kan Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Alaka Da Boko Haram

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty Internional ta ce ta damu matuka akan zamen shari'ar da aka soma yiwa dubban mutanen da ake zargi da alaka da kungiyar boko haram a Nijeriya.

A ranar Litini data gabata ne aka fara gurfanar da mutanen a cibiyoyin tsaro na soji dake Kainji a jihar Neja, da kuma wasu a barikin soji na Giwa dake birnin Maiduguri a jihar Borno dake arewa masi gabashin kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da ake yi wa mutane da suka kai irin wannan adadi shari'a kan zargin alaka da kungiyar Boko Haram

Kungiyar ta bakin darectan ta a Nijeriya Osai Ojigho ta ce babban abun damuwa ne kasancewar ana gudanar da zaman a asirce ba tare da halartar jama'a da manema labarai ba.

Hukumomin shari'a dai sun ce an hana jama'a da 'yan jarida halartar zamen saboda dalilai na tsaro.

Kimanin masu zargin dubu da dari shida ne aka soma yi ma shari'a a farkon wannan mako a wasu cibiyoyin tsaro, kafin daga bisani kuma sauren su kimanin 5,000 a yi musu nasu shari'o'in.

Oct 11, 2017 15:55 UTC
Ra'ayi