• Gargadin Asusun Bada Lamuni Dangane Da  Koma Bayan Tattalin Arzikin Afirka

Asusun Bada Lamunin ya ce; tattalin arzikin nahiyar ta Afirka zai iya samun koma baya.

Rahoton da asusun ya fitar akan tattalin arzikin duniya, ya ce; acikin wannan shekarar ta 2017 ci gaban kasashen Afirka da ke kudancin sahara ba zai kai daraja 2 da digo shida cikin dari ba.

Rahoton ya ce; koma bayan tattalin arziki da aka samu a cikin kasashen Najeriya da Afirka ta kudu shi ne zai shafi kasashen na arewa da sahara. Sai dai rahoton ya yi hasashen cewa a cikin shekarar 2018 mai zuwa, tattalin arzikin kasashen zai sami ci gaba da daraja 3. 4%.

Wani sashe na rahoton ya ce ci gaban tattalin arzikin nahiyar ba ya tafiya kafada da kafada da yawan al'ummar da ke cikin nahiyar.

Kasashen Najeriya da Angola na daga cikin na gaba wajen samar da man fetur a cikin nahiyar, ana kuma sa ran cewa a cikin wannan shekarar ta 2017 tattalin arzikin Najeriya da ya sami koma baya  zai farfado.

Raguwar farashin man fetur a kasuwannin duniya wanda ya fara a 2014 ya shafi tattalin arzikin Najeriya.

 

Tags

Oct 12, 2017 06:29 UTC
Ra'ayi