• Fira Ministan Kasar Moroko Ya Yi Barazanar Yin Murabus Daga Kan Mukaminsa

Fira ministan kasar Moroko ya yi barazanar yin murabus daga kan mukaminsa sakamakon bullar sabani da rikici a cikin jam'iyyarsu mai mulki a kasar.

Jaridar Ra'ayin Yaum ta habarta cewa: Fira ministan Moroko, kuma babban sakataren Jam'iyyar Justice and Development Party mai mulki a kasar Sa'aduddeen Usmani ya yi barazanar yin murabus daga kan mukaminsa musamman bayan kakkausar suka da yake fuskanta daga bangaren magoya bayan tsohon fira ministan kasar.

A taron Jam'iyyar ta Justice and Development Party da aka gudanar a garin Meknes da ke arewacin kasar Moroko: Fira minista Sa'aduddeen Usmani ya yi furuci da cewa: Yana shirye ya yi murabus daga kan mukaminsa matukar hadin kan jam'iyyar yana fuskantar hatsari saboda kasancewarsa kan mukaminsa.   

Tags

Oct 12, 2017 11:53 UTC
Ra'ayi