• Mahukuntan Masar Sun Tsawaita Dokar Ta Bacin Da Aka Sanya A Kasar

Mahukutan kasar Masar sun sanar da tsawaita dokar ta bacin da aka kafa a kasar har na tsawon watanni uku masu zuwa a kokarin da gwamnatin take yi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wata majiyar tsaron kasar Masar din tana fadin cewa a yau Alhamis ne gwamnatin kasar Masar din ta sake tsawaita dokar ta bacin na tsawon watanni uku masu zuwa a duk fadin kasar.

A watan Aprilun da ya gabata ne dai gwamnatin Masar din ta sanar da kafa dokar ta bacin bayan wani harin ta'addanci da aka kai wasu cocuna guda biyu a kasar da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 45 a kasar, sannan kuma Yunin da ya gabata ne aka sake tsawaita dokar har na tsawon watanni ukun.

Kasar Masar din dai tana fuskantar hare-haren ta'addanci a kasar musamman a yankin Sina inda 'yan ta'addan kungiyoyin takfiriyya suke ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro da sauran fararen hula na kasar.

 

Oct 12, 2017 17:23 UTC
Ra'ayi