• An Haramta Yin Zanga-Zanga A Wasu Biranen Kasar Kenya Gabannin Zaben Shugaban Kasa

Ma'aikatar cikin gidan kasar Kenya ta haramta yin zanga-zanga a birnin Nairobi da wasu fitattun wajaje na kasar a kokarin da ake yi na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali kafin zaben shugaban kasar da ake sa ran za a sake gudanarwa nan gaba kadan.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar hukumcin haramcin da aka fitar a yau Alhamis ya hada da tsakiyar birnin Nairobi, babban birnin kasar, da garin Kisumu haka nan da kuma garin bakin ruwan nan na Mombasa wajajen da ake ci gaba da zanga-zangogi tun bayan da kotun koli ta kasar ta soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Augustan da ya gabata.

To sai dai babban jam'iyyar adawa ta kasar, wacce ta ke ta gudanar da gangamin ganin an gudanar da kwaskwarima ga dokokin zaben da kuma korar jami'an da suka gudanar da wancan zaben, ta ce ba za ta girmama wannan hukuncin ba don kuwa za ta ci gaba da zanga-zangar da ta kira a yi a gobe Juma'a.

A ranar 26 ga watan Oktoban nan da muke ciki ne dai ake sa ran za a sake zaben shugaban kasar kamar yadda dokokin kasar suka tanada bayan da kotun kolin ta soke zaben da aka gudanar a watan Augustan da aka sanar da shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe.

 

Tags

Oct 12, 2017 17:24 UTC
Ra'ayi